<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><lyrics>[V1]
 1) Hosanna ga Ɗan Dawuda! Mai albarka ne shi
 Wanda ke zuwa cikin sunan Ubangiji.
 Kai Sarkin Isra'ila, shafaffen Allahnmu,
 Cikin sunan Maɗaukaki, ka zo ka cece mu.

[V2]
 2) Hosanna ga Ɗan Dawuda! Mai albarka ne shi
 Wanda ke zuwa cikin sunan Ubangiji.
 Mutanen da sun ɗiba gazarin dabino,
 Sun shimfiɗa a hanyarka domin ka taka su.

[V3]
 3) Hosanna ga Ɗan Dawuda! Mai albarka ne shi
 Wanda ke zuwa cikin sunan Ubangiji.
 Yau dukan jama'arka sun kawo yabonsu,
 Domin su gai da sarkinsu wanda ya fanshe su.

[V4]
 4) Hosanna ga Ɗan Dawuda! Mai albarka ne shi
 Wanda ke zuwa cikin sunan Ubangiji.
 Ka shiga Birnin Ƙudus, ya kai mai nasara,
 Tawali'u da yardar rai sun kai ka mutuwa.

[V5]
 5) Hosanna ga Ɗan Dawuda1 Mai albarka ne shi
 Wanda ke zuwa cikin sunan Ubangiji.
 Loton da ka ke duniya, wahala ce ka sha,
 A hannun daman Allah, aka ba ka ɗaukaka.

[V6]
 6) Hosanna ga Ɗan Dawuda! Mai albarka ne shi
 Wanda ke zuwa cikin sunan Ubangiji.
 Ya Yesu Almasihu, Allah Maɗaukaki,
 Kai ne Mai Ceton duniya, ya kai Mai Tsarki.</lyrics>
<title>Hosanna Ga Ɗan Dawuda! Mai Albarka Ne Shi LW95</title>
<hymn_number>95</hymn_number>
</song>